Talata 7 Yuli 2026 - 23:19
Shahadar Sayyid Khamenei Babban Rashi Ne Ga Al’ummar Musulmin Duniya 

Hauza/ Dandalin Resource na Harkar Musulunci a Najeriya ƙarƙashin jagorancin Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bayyana shahadar Shahidin Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, a matsayin babban rashi ga al’ummar Musulmi a faɗin duniya, yana mai jaddada cewa rayuwarsa ta kasance cike da imani, hidima, adalci da kuma jagoranci mai tsayin daka.

A cewar rahoton wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, shugaban Resource Forum, Farfesa Abdullahi Danladi, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Litinin, inda ya miƙa ta’aziyya bisa rasuwar Ayatullah Sayyid Ali Khamenei kafin gudanar da jana’izarsa da aka tsara yi ranar 9 ga Yuli, 2026, bayan kammala jerin tarukan tunawa da shi a Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasar Iraki.

Farfesa Danladi ya bayyana cewa shahadar manyan malamai da shugabanni masu riƙe da manufa ba kawai tana haifar da giɓin shugabanci ba ne, har ma tana barin babban gibi a fannin ɗabi’a da ilimi a cikin al’umma.

Ya ce Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa addinin Musulunci hidima, neman tabbatar da adalci, da kuma kare mutunci da ‘yancin kai na al’ummar Iran.

A cewarsa, tsawon shekaru sama da talatin da suka gabata, Sayyid Khamenei ya jagoranci Jamhuriyar Musulunci ta Iran a cikin manyan ƙalubalen siyasa, tattalin arziki da tsaro. Ya bayyana cewa duk da takunkumai, barazana da matsin lamba daga ƙasashen waje, ya ci gaba da tsayawa kan manufofinsa tare da kare abin da yake ganin haƙƙin al’ummarsa da kuma waɗanda ake zalunta.

Farfesa Danladi ya ƙara da cewa jajircewa, ƙuduri da tsayin dakan Sayyid Khamenei wajen bin gaskiya sun sa ya samu girmamawa da karɓuwa fiye da iyakokin Iran.

Ya bayyana cewa tarihi ba ya tuna shugabanni kawai saboda mukaman da suka riƙe ba, sai dai saboda manufofin da suka tsaya a kai. Ya ce mutane da dama za su ci gaba da tunawa da Sayyid Khamenei a matsayin alamar juriya, ƙin mamaya da kuma imani da cewa Musulunci na da ikon jagorantar al’umma wajen fuskantar ƙalubalen zamani.

Da yake ambaton aya ta 185 a cikin Suratul Ali Imran, Farfesa Danladi ya tunatar da musulmi cewa: “Duk mai rai zai ɗanɗani mutuwa.” Ya bayyana cewa mutuwa wata hanya ce da babu wanda zai tsira daga gare ta.

Ya ce abin da ke bambanta mutum ba mutuwarsa ba ce, sai dai ƙimomin da ya rayu a kansu da kuma abin kirki da ya bari a baya. Ya ƙara da cewa: “Kamar yadda muka ƙaunaci Sayyid Ali Khamenei, Allah Ya fi mu ƙaunarsa. Don haka muna miƙa wuya ga hukuncin Allah cikin haƙuri da imani.”

Farfesa Danladi ya miƙa ta’aziyya ga jagoranci da al’ummar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, iyalan marigayin, jagoran Harkar Musulunci a Najeriya Sheikh Ibraheem Zakzaky, al’ummar Musulmi ta duniya da kuma duk waɗanda suka samu ƙarfafuwa daga rayuwa da jagorancin Sayyid Khamenei.

Ya kuma roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya karɓi ayyukan hidimar da Sayyid Khamenei ya yi wa addini, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya ba shi matsayi mafi girma a Aljanna, sannan Ya bai wa duk masu jimamin rashinsa haƙuri da juriya.

A ƙarshen jawabinsa, Farfesa Danladi ya sake ambaton aya ta 156 a Suratul Baƙara: “Lalle daga Allah munke, kuma gare Shi za mu koma.” Ya yi addu’ar Allah Ya sanya abubuwan alheri da marigayin ya bari su ci gaba da kasancewa tushen shiriya da abin koyi ga al’ummomi masu zuwa.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha